Wata kungiyar fararen hula mai rajin tabbatar da tsaro da kare dimokradiyya, wacce ake kira Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria, ta shirya wasu jerin zanga-zanga a London don nuna adawa da zuwan Shugaba Muhammadu Buhari birnin.
Shugaban na Najeriya ya isa London ne a tsakiyar mako nan, inda ya je a duba lafiyarsa kamar yadda fadar gwamnatin Najeriya ta fada.
Amma masu shirya zanga-zangar sun ce kasancewar Buhari a London ya saba alkawarin da ya yi cewa ba zai nemi magani a kasashen waje ba.
A cewarsu, hakan na nuna rashin amincewarsa da tsarin kiwon lafiyar kasarsa.
Sun kuma kara da cewa rashin kayan ayyukan likitocin Najeriya na nuna gazawarsa wajen inganta samar da kiwon lafiya.
Shugaban tsare-tsaren kungiyar, Frederick Odorige ne ya fadawa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey, cewa masu shirya zanga-zangar za su roki hukumomin Burtaniya da su hana Buhari da sauran manyan jami’an gwamnati zuwa asibitocin kasar.