Kungiyoyin sunce sun yi wannan yunkurin ne saboda suna nema a tsige Shugaba Goodluck Jonathan akan cewa bai yi wa kasa aikin komai ba tunda aka zabe shi.
Kungiyoyn sun jera laifukan da suke zargin shugaban kasar da aikatawa da suka hada da rashin cika alkawuran da yayi dangane da samar da wutar lantarki, da yaki da cin hanci da rashawa, yawan yajin aiki da ma’aikata ke yi, da kuma kin aiwatar da kasafin kudi.
Sai dai a nasu bangaren, jami’an gwamnati sun ce tunda ake shugabanni a Najeriya ba a taba samun wanda yayi aiki irin Shugaba Goodluck Jonathan ba.
A cikin hirarsu da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda, kwamred Isa Tijjani, shugaban hadakar kungiyar yayi karin haske dangane da wannan yunkurin.