Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu A Landan Ta Umarci Lauyan Ibori Da Ya Biya Dala Miliyan 36


James Ibori
James Ibori

A ranar Litinin ne wata kotu a Landan ta umarci tsohon lauyan tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur, James Ibori ya biya kusan fam miliyan 28 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 36 saboda ya taimaka wajen boye kudaden da aka samu ba bisa ka'ida ba.

An sami Bhadresh Gohil da laifuka 13 a shekara ta 2010 da suka hada da zambar kudade da kuma wasu laifuka da suka shafi taimakawa Ibori, wanda ya kasance gwamnan jihar Delta a kudancin Najeriya daga 1999 zuwa 2007, da boye kudaden da aka samu ta hanyar aikata laifuka.

A cikin wata sanarwa da ofishin shigar da kara na Burtaniya CPS ya fitar, Gohil wanda aka yankewa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, kuma ya cika rabin hukuncin da aka yanke masa, a ranar Litinin din da ta gabata an umarce shi da ya biya sama da fam miliyan 28, ko kuma ya fuskanci hukuncin daurin shekaru shida.

Matakin dai na zuwa ne bayan Ibori wanda ya yi amfani da matsayinsa ba bisa ka'ida ba don arzurta kan sa tare da wawure miliyoyin kudade a Birtaniya da sauran wurare, a ranar Juma’a an yanke masa hukuncin biyan Fam miliyan 101.5 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 130 ko kuma ya fuskanci hukuncin daurin shekaru takwas.

Ibori wanda yanzu haka yake a Najeriya ya ce zai daukaka kara.

Umurnin kwace kadarorinsa shi ne na biyu mafi girma da aka yi a karkashin dokar mallakar haramtattun kudade ta Biritaniya ta 2002 tun lokacin da ta fara aiki, a cewar bayanan da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu daga hukumar CPS a karkashin dokar 'Yancin ba da Bayanai.

Tarin kwace kadarorin ya kwashe tsawon shekaru goma tun lokacin da aka yanke wa Ibori hukunci saboda dadewar da aka yi a kotu da kuma takaddamar shari'a a Landan.

"Za'a mayar da kudaden Ibori ga gwamnatin Najeriya" in ji Kwamandan NCA reshen Suzanne Foster.

A shekarar 2021, Biritaniya ta dawo da Fam miliyan 4.2 da aka kwace daga hannun tsohuwar matar Ibori da ‘yar uwar sa, wadda ita ma ta yi zaman gidan yari saboda taimaka masa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG