Arangama jefi jefi sun ci gaba da faruwa jiya Lahadi kwana uku a jere ke nan domin mamaye birnin Ghanzi dake kudu maso gabashin kasar Afghanistan, a yayinda aka samu ikirarin da suka sabawa juna akan ko gwamnati ce ko kuma yan Taliban ne ke iko da muhimman wurare.
Hafsan sojojin kasar Janaral Mohammed Sharif Yaftail, ya fadawa wani taron ‘yan jarida jiya Lahadi a birnin Kabul cewa, sojoji suna maida martanin fatattakar yan Taliban daga birnin.
Janaral Yaftail ya ce sojoji ke iko da muhimman wurare a Ghazni ciki harda ofishin gwamnan lardin da hedkwatar da yan sanda da gidan yari da kuma ofishin hukumar liken asirin kasar.
Jami’an asibiti da mazauna birnin dake arcewa sun fadawa yan jarida cewa an kai fiye da gawarwakin sojoji da yan sanda Afghanistan dari asibiti, kuma asbitin na da karancin wuren adana gawarwaki
Facebook Forum