Wani kakakin hukumar ya fada jumma’a cewa jami’an kasar Saudiyyan ne suka tabbatarda mutuwar karin mutanen. Ya kara da cewa an sami sabon mutum daya da ya kamu da cutar cikin kasar a yankin da ake kira Al-Ahsa, wanda ya kawo jumlar wadanda cutar ta harba a fadin duniya baki daya ciki harda wadanda suka rasu, zuwa hamsin.
A bara aka gano cutar. Rabin wadanda larurar ta kama sun fito daga kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an sami rahotannin cutar a kasashen da suke gabas ta tsakiya, da suka hada da Jordan da Qatar, da Tunisia, da kuma a turai.
A farkon makon nan wani mutum dan shekaru 65 da haifuwa a faransa ya mutu sakmakon kamuwa da cutar, shine mutum na farko da cutar ta halaka a kasar.
Kwayoyin cutar suna haddasa tari, da zazzabi da kuma pneumonia, kuma ana iya kamuwa da cutar idan aka kusanci wanda yake dauke da kwayoyinta sosai.