Dutsen da aka lakabawa suna mai lambar 1998 QE2 bai yi barazana ga duniyarmu ba domin nisan ta inda ya wuce da duniyar mutum kusan kilomita milyan uku ne, kamar nisan duniya zuwa wata har sau 15.
Masana kimiyya da suke aiki a hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka suka ce sunan da aka lakabawa wannan dutsen bashi da wata dangantaka da wani abu a doron kasa.
Sunayen da ake baiwa irin wadan nan duwatsu sun hada harda shekarar da aka fara gano su, da wata da kuma wace rana a cikin watan da aka gano shi.
Labaran irin wannan gilmawar suna taimakawa wajen kara fadakarda jama’a irin wadan nan duwatsu dake suke wucewa kusa da duniyar mutum.