Wadannan mata da suka fito daga wurare daban daban sun koka game da kame ’yan kungiyar da suka ce jami’an sojan sun yi da wasu kuma da suka kasance mazajensu da har yanzu ba a ji duriyarsu ba.
A cewar wasu daga cikin matan, sun kwashe sama da shekaru goma ba su ji duriyar ‘ya’yansu ba, wadanda suka hada da ‘yan kasuwa da dalibai daga makarantu daban daban wasu ma magidanta ne, lamarin da ya kai iyayen yaran ga kafa wata kungiya da ake kira “Jira Dole” domin fafutukar nema ‘ya’yan nasu da ma mazajensu.
Wasu matan sun tattauna da wakilin Sashen Hausa inda suka bayyana matukar damuwa kan halin da suka fada biyo bayan rashin ganin ‘ya’yansu da mazajensu. Zahra Amadu Aji tana cikin matan da suke kira ga hukumomi wadda ta bayyana damuwa yayin da take kuka.
Ta ce “Mun zo neman taimako saboda rayuwar mu ta kasance cikin wahala, ni da farko na yi aure kwana 28 an fitar da mijina, an rike shi a bariki ban sake jin labarinsa ba sai labarin rasuwar shi. Bayan shekara biyar na sake yin wani aure baban wannan yara, da safe ya ce zai je kasuwa ya dawo. Shi kuma an kama shi, ya bar mana ‘ya’ya 12 da ni da kishiyata.”
Wata mata da ta zanta da sashen Hausa ta ce an kama danta mai shekaru 30 da haifuwa har yanzu ba ta ji labarinsa ba; yau kusan shekaru takwas kenan. Ta ce tana rokon gwamnati da masu taimako da su taimaka mata ta gane ko danta na raye ko kuma bashi a raye.
Shugabar gidauniyar Al Amin mai fafutukar kare hakkin mata, Hajiya Hausatu Al Amin ta bayyana bukatun matan. Ta ce suna bukatar a bayyana musu alkalumman adadin yara da aka kama a Maiduguri, guda nawa suka mutu a ciki kana guda nawa suke raye.
Ta kuma ce suna kira ga gwamnatin tarayya da ta bada jawabi a kan wani rahoto na musamman da aka fitar a kan abubuwa da suka faru a jihar su ta Borno. Ta kara da cewa suna kuma bukatar jawabi game da rahoton kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa a kan abubuwa da suka faru a Borno, inda wadannan mata suka je suka bada bahasi.
Daga Maiduguri ga rahoton wakinlinmu Haruna Dauda Biu: