Kungiyar kwallon zari ka ruga ta Denver Broncos, ta doke takwararta ta Carolina Panthers da ci 24 da 10, ta lashe kofin Super Bowl na zakarun wannan wasa wadda a nan Amurka ake kira kwallon kafar Amurka.
Duk da cewa ‘yan tsaron bayansu sune na daya a duk kakar kwallon bana, masana sun yi hasashen cewa ‘yan wasan na Denver Broncos zasu sha kashinsu a hannun ‘yan Carolina Panthers, wadanda suke da maciya kwallo ka’in da na’in karkashin madugunsu Cam Newton, wanda kwana daya kafin wannan wasa, aka ayyana shi a zaman gwanin gwanayen wasan kwallon kafar Amurka na wannan shekara.
Amma ‘yan tsaron gida na Denver Broncos, sun yi ta caa a kansa suka hana shi sakat, Sau bakwai ‘yan tsaron bayan na Denver Broncos sun a kaiwa ga Cam Newton, suna kayar da shi har kasa, abinda ba a taba yins aba a tarihin wannan gasa ta cin kofin Super Bowl.