Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bashar Aliyu Mai Zanen Motocin Zamani Ya Fuskanci Matsaloli Da Dama


Bashir Aliyu Mai zanen motoci
Bashir Aliyu Mai zanen motoci

Bashar Aliyu ya hadu da matsalaloli na rayuwa tun a gida, sanadiyar yana yini zane-zane kuma yana kwana zane, idan yana zane-zanen sa na motoci a cikin dare a tsorace yake yi, saboda iyayen shi basu so yanayi. kasancewar idan kakar shi ta fito taga hasken fitilar dakin shi to bazata iya bacci ba. Don takan rinka yimasa fada sai tace "Har yanzu kana nan kana shiriritar ka, sai safiya tayi a rinka tada kai zuwa makaranta ka ki tashi ko?'' shi yasa da yaji motsinta zai kashe fitilar sa har sai ta koma dakin ta sannan yaci gaba da aikin shi.

Amma daga karshe da ta fahinci yadda abin yake, sai ya kasance tafi kowa taimakon shi ga wannan baiwar da Allah ya bashi, Bashar ya hadu da matsalar rashin kudi, da tsana da kushe ga wadan su mutane da wadan su abokai ke yi masa. Kuma suna cewa mashiririci ne baida aikin yi, shi yasa yake wannan zanen banza, suna fadin hakan a gaban sa don ransa ya baci, haka kuma tun a makaranta yasha haduwa da matsaloli daban-daban, sanadiyar ko a makaranta aikin sa kawai zane-zane a cikin littattafan sa. Wajen kuma ganin cewa ya samu ci gaba a baiwar shi, yayi hasarar wasu zane-zanen sa da ya bawa wadanda ke cewa zasu taimaka mishi kuma abin yaci tira.

Bashar, ya sha gwagwarmaya wajen tuntubar kamfanonin motoci a yanar gizo (Internet) da Hausa, ya sha tafiyar kasa daga anguwar su Runjin Sambo zuwa Gawon Nama domin shiga café kullun, ya dau tsawon shekara 6 yana hakan domin ganin cewa ya cimma gurin sa da yake dashi.

Haduwar Bashar da Jelani Aliyu ya kara masa kwarin gwiwa sosai, saboda yana yaba aikin shi, kuma shine wanda yayi mai iso zuwa ga gwamnan jihar sakkwato, kuma gwamnan ya san dashi, daga karshe gwamnan ya bashi damar ya nemi gurbin karatu a kasar Amurka wanda gwamnati zata biya mishi karatun shi baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG