Kungiyar kwallon kwando ta Nigeria’s D-Tigers ta yi nasara kan Dominican Republic da ci 89-87 a San Domingo, yayin da kungiyar ta ke kara matsa kaimi wajan shirye shirye, kofin kwallon kwando na FIBA na duniya da za’a yi a China cikin watan Augusta.
Mai horaswa, Alex Nwora, ya ce ‘yan wasansa sun mamaye wasan da aka yi gumurzu sosai.
Kamfanin dillanci labarai na Najeriya NAN ya fada tun a ranar Asabar da ta gabata cewar Nigeria’s D Tigers ta yi nasara akan Dominican Republic, wadda ta na daya daga cikin wadanda suka buga gasar cin kofin kwallon kwando na duniya, da ci 85-81 a wasan farko a wasan sada zumunci da suka buga.
Nwora ya ce wasannin gwajin zai bashi dama ya auna ‘yan wasansa a yanayin irin wasansu da kuma jarraba sabbin dabaru.
‘Yan kwanakin nan da suka gabata sun kasance masu ban sha’awa sosai a sansanin horarwar mu. Saboda ‘yan wasan mu sun nuna sha’awarsu na su koyi sabbin abubuwa da kuma karin da’a a lokacin wasan.
“Wasannin sada zumuncin za su taimakawa masu horarwa wajen tantance ‘yan wasa a cewar Nwora.
Facebook Forum