Karawar na zuwa ne, kwanaki bayan da Manchester United ta hau saman teburin gasar da maki 36 bayan da ta doke Burnley da ci 1-0 a farkon makon nan mai karewa.
Idan Manchester United ta yi nasarar lashe wannan wasa wanda za a yi a filin was a na Anfield, za ta ba Liverpool tazarar maki shida kenan.
Ita dai Liverpool ita ce ke rike da kofin gasar, amma kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce karawar ta ranar Lahadi, za ta ba kungiyarsa damar auna ko su gwanaye ne a gasar ta Premier League.
Darewa saman teburin gasar ta Premier da Manchester United ta yi, shi ne na farko tun bayan da Sir Alex Ferguson ya daina horar da kungiyar – wato tun a kakar wasa ta 2012-13.
Nasarorin da Manchester ke samu, na zuwa ne bayan da ta buga wasanni 11 a jere ba tare da an doke ta ba tun da aka fara wannan a watan Nuwamba.
Ita dai Liverpool wacce ke rike da kofin gasar, ba ta rasa wasa ko daya a gida ba tun bayan kayen da ta sha a hannun Crystal Palace a watan Afrilun 2017.