Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mutu Ya Kashe Mutane 26 a Wata Mijami'a cikin Jihar Texas Nan Amurka


Mijami'ar da aka kai harin a garin Sutherland Springs dake jihar Texas
Mijami'ar da aka kai harin a garin Sutherland Springs dake jihar Texas

Wani mutum da aka yi imanin an kore shi daga rundunar sojan sama, ya bude wuta a wata Majami’a dake kusa da birnin San Antonio na jihar Texas da safiyar jiya Lahadi, inda ya kashe masu bauta 26 da raunata wasu a kalla 20.

Mutanen da wannan mummunan harin bindigar ya shafa sun hada daga ‘yan shekaru biyar zuwa saba’in da biyu.

Shi ma ‘dan bindigar na daga cikin wadanda suka mutu, babu masaniya kan abin da ya haifar da wannan lamari.

Masu bincike na gwamnatin tarayya da suka hada da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da hukumar sa ido kan barasa da taba da kuma bindigogi duk suna garin Sutherland Springs na jihar Texas, mai tazarar kilomita 50 daga birnin San Antonio, suna gudanar da bincike.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira wannan harbi a matsayin “aikin rashin imani” kuma yayi kira da ayi musu addu’a. shugaban dai na bibiyar halin da ake ciki daga kasar Japan, kasar da ya fara yada zango a ziyarar kasashe biyar da yake a yankin Asiya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG