Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Likitan Hakori A Italiya Ya Yi Yunkurin Bada Hannun Roba Don Karban Allurar Rigakafin Covid


Wani likitan hakori a Italiya na fuskantar yiwuwar tuhumar aikata laifuka bayan ƙoƙarin karɓar rigakafin cutar coronavirus a hannun jabun da aka yi da 'silicone' na roba.

Wata ma’aikaciyar jinya a birnin Biella da ke arewacin kasar, Filippa Bua, ta ce nan da nan ta gano saboda jikinta bai bata ba yayin da wannan mutum ya mika hannunsa don karbar allurar a ranar Alhamis.

"Lokacin da na gano hannun, na ji fatar da sanyi da kuma gumi, kuma launin fatar ya yi haske sosai," Bua ta shaida wa jaridar Italiya Corriere della Sera.

Ta ce da farko ta yi tunanin mutumin mai shekaru 57 yana da irin hannun roban ga ake sa wa wandanda aka yanke masu hannu ne kuma ya yi kuskuren bayar da hannun da bai dace ba. Tuni ta daga rigarsa ta gano hannun silicone roba.

“Nan da nan na fahimci cewa mutumin yana kokarin gujewa allurar ne ta hanyar amfani da hannun roba ta silicone, inda yake fatan zan yi masa allurar, ba tare da sani na ba,” in ji Bua.

Ma’aikacin jinyar ta ce mutumin ya yarda cewa ba ya son allurar rigakafin amma kuma yana nema samun takardar izinin tafiya wurare daban-daban”, wanda daga ranar Litinin za a bukaci amfani da takardar shiga gidajen cin abinci, sinima, da dai sauran wuraren shakatawa a Italiya.

Tuni dai aka dakatar da shi daga aiki saboda kin yin allurar da Italiya ke bukata ga duk ma'aikatan lafiya.

Ma’aikaciyar jinyar ta ce mutumin ya kasance mai ladabi kuma ya bar cibiyar allurar bayan yunkurin da ya kasa yi.

XS
SM
MD
LG