Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda Yana Fafatukar Kare Iyali A Dandalin Sada Zumunta


SP Bright Edafe
SP Bright Edafe

Rundunar ‘yan Sandan jihar Delta ta yi kira ga wadanda ake cin zarafin su a gidajen aure, musamman mata su kai kara a ofishin ‘yan Sanda mafi kusa a maimakon yin korafi a dandalin sada zumunta.

Kakakin rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Delta SP Bright Edafe ya bada wannan shawarar ne a dandalin sada zumunta X da yake maida martani a kan hoton wata mace da aka kafa a dandalin sada zumunta na rundunar ‘Yan sandar jihar Delta, na wata mace da fuskarta a kumbure da bandeji jina-jina da aka ce maigidanta ne ya lakada mata duka, kuma ‘yan sanda basu dauki wani mataki ba.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Delta ya maida martani a shafinsa na X cewa,

Kina auren wani mutum a Asaba yana dukanki kullum, kina da 'yan uwa, kina da abokai; kuma kuna da ofisoshin ‘yan sanda sama da shida a Asaba. Kun ki kai karar shi, amma kun gwammace ku zo kan dandalin sada zumunta X don ku yi kuka ga ’yan sanda su zo su taimaka.

Kakakin rundunar “yan sandan ya shawarci mata su rika zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su, domin kai rahoto, kada su saurari abokansu da zasu kashe masu guiwa da cewa, "Wannan Najeriya ce”. Ya ce babu abinda ya alakanta Najeriya da rashin kai rahoto ofishin ‘yan sanda.

Ba wannan ne karon farko da SP Bright Edafe ya ke wallafa shawarwari da su ka shafi aure da zaman gida ba. A wani lokaci baya ya ba mata shawara cewa,

"Ya kamata iyaye mata su san hakkin su , ba za a iya raba yaro a kasa da shekaru shida (6) daga mahaifiyar ba. Iyaye mata ne ya kamata asu rike yaro duk lokacin da iyayen suka rabu. Sai dai idan akwai ciwon hauka. Maza da iyalan uba sukan zalunci mata da iyaye mata su kwace yara daga hannun uwa. Wannan kuskure ne. Idan kin sami kanki a cikin wannan halin, 'yan sanda na iya zama muryar ki, ko da yake yanke hukuncin wanda zai kula da yara yana hannun kotu, doka ta ce, mahaifiya ta kula da yaron da ya ke kasa da shekaru shida. Ku san hakkin ku."

SP Bright Edafe , ya kuma ba wadanda ba su yi aure ba shawara kan abinda ya kamata su yi la'akari da shi lokacin da su ke neman aure.

"Samari da 'yan mata, kafin ku yi aure, ku tuna cewa, yaranku na gaba ba su da damar yanke shawarar ko wacece za ta zama mahaifiyarsu ko mafinsu. Ku ne za ku yanke wannan shawarar . Don Allah a yi abin da ya dace ta hanyar ba su uwa ko uba nagari. Ba wai kawai yadda ku ke ji ba."

DOMIN IYALI: Bincike Kan Cin Zarafin Mata A Gidan Aure, Mayu 02, 2024.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:16 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG