Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu ya Rikito


Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, tace kawo yanzu mutane akala takwas ne aka ceto daga wani hatsarin jirgin sama mai saukar Ungulu, daya rikito a wani yankin tafkin birnin Lagos.

Wakilin muryar Amurka, Babangida Jibrin wanda ya ziyarci yankin na Oworon Shoki, inda hatsarin ya faru ya ruwaito cewa jirgin na dauke da mutane goma sha biyu ne amma an samu ceto mutane takwas inda aka samu gawawwaki hudu inda kuma har yanzu ba,a gano mutane biyu ba.

Kakakin hukuma kula da filayen jiragen sama na Najeriya, Mr. Yakubu Datti,yace jirgen na wani Kamfani mai suna Bristol Helicopter ne dake zirga zirga tsakanin yankin kudancin Najeriya, zuwa birnin Lagos.

Binciken da muryar Amurka, ta gudanar yana tabbatar cewa wadanda suka rasu ma’aikatan wani kamfanin hakar mai ne dake yankin kudu maso kudancin Najeriya, inda kuma jirgin da ya dauko su ke kan hanyarsa zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Lagos, kuma ana saura minti biyar wannan jirgi ya sauka ne ya rikito.

XS
SM
MD
LG