Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Sanda Ya Amshi Haihuwa Kafin A Je Asibiti


Wani dansanda a kasar Amurka ya tsayar da wata mota tana kan ta tafiya kamar yadda kyammarar sa ta gaban mota mai daukar hotannin bidiyo ta dauka, wanda a yanzu kusan dukkan 'yan sanda kan yi anfani da irin wannan na'urar daukar hotanni domin nuna irin aikin da ko wane jami'in tsaro ke yi.

kamar yadda ofishin 'yan sandan ya ruwaito, dan sandan mai suna Anthony Reynolds ya tsayar da motar ne a yayin da ya ga matukin motar na ta sharara gudu har ma yana wuce jar danja mai tsayar da motoci akan hanya wato Red Light a turance.

Kamar yadda doka ta tanada a kasar Amurka, idan jami'in tsaro ya tsayar da mota, matukin motar zai faka motar kuma ya sauke gilashin motar sannan ya zauna ciki har sai lokacin da jami'in da ya tsayar da shi ya zo inda ya ke sa'annan ya bayyana masa dalilin tsayar da shi.

Allah sarki! sai kawai matukin wannan mota ya bude kofa ya daga hannuwan sa sama ya da kafi ya ce, "matata ce zata haihu, tana cikin nakuda". nan da nan sai jami'in tsaron ya kira motar bada taimakon gaggawa wato abulance a turance, amma kafin motar ta iso wasu abokan aikin jami'in tsaron sun garzayo zuwa wurin.

Suna zuwa sai kawai suka iske matar har ta haihu a mota ga shi kuma motar da suka kira bata iso ba. Dan sanda Anthony ya yi maza maza ya dauki 'yar jaririyar da ke ta kokarin yin lumfashi ya share mata hanci ya kuma taimakawa mahaifiyar tamkar wani likita kafin motar kai daukin gaggawar ta karaso.

Wacce irin rawa 'yan sandar kasar ku suke takawa wajan taimakawa jam'a? ku bayyana mana ra'ayin ku ta shafin mu na dandalin voa facebook.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG