Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bala'in da 'Yan Boko Haram Suka Haddasa


'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram suna karban kayayyakin agaji
'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram suna karban kayayyakin agaji

Bala'in da 'yan Boko Haram suka haddasa a arewa maso gabashin Najeriya, ya sa mutane da yawa sun rasa rayukansu. Wasu da dama sun jikata inda wasu kuma suka rasa muhallansu.

Har ila yau akwai wadanda suka tagayyara, Wasu kuwa kidime wa suka yi saboda abubuwan da suka gani da muguwar azaba da suka sha.

Rikicin addini da na kabilanci sun taimaka wajen haddasa wahalhalun da jama'a ke fuskanta da kuma ambaliyar ruwa a wurare daban daban da kashe-kashe da kone-kone. wanda yayi sanadiyar raba wasu yara da iyayensu har abada.

Saboda shirin ko ta kwana kungiyoyin jin kai da masu tallafawa jama'a, ya sa suna neman taimako daga kowa suna tarawa domin kawo taimako yayinda ake bukata. A Najeriya akwai kungiyoyi da dama da suke fadakar da jama'a mahimmancin bada tallafi idan aka bukacesu su yi hakan.

Yau a Jamhuriyar Nijar kungiyoyin bada agaji zasu taru su kawo fadakarwa akan wannan ranar. Rana ce kuma ta tunawa da wadanda suka sadakar da kansu domin su kawowa wasu agaji.

Misali a jihar Maradi akwai gungiyoyi da dama da suke kawo agaji musamman ga wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu da ambaliyar ruwa da kuma rikicin kabilanci.

Aikin agaji na fuskantar wasu matsloli, inda mutane sukan sa son rai. Idan wasu sun shiga wata matsala aka kawo masu agaji sai wadanda basa cikin wata damuwa su ce dole su ma a tallafa masu. Wasu kuma na ganin masu hannu da shuni ne kawai ya kamata su bada agaji. Lamarin ba haka yake ba. Da kwabo kwabo za'a tara miliyoyi yadda zasu iya taimakawa. Wato haki ne akan kowa ya bada agaji komi kankanta.

XS
SM
MD
LG