Ranar juma'ar da ta gabata ne aka kori wani jami'in dan sanda mai suna kofur Musiliu Aremu daga aiki a sakamakon zargin sa da aikata kisan kai akan wasu ma'aurata su biyu Mr Godwin Ekpo da matar sa a yankin Ijegun , Alimosho dake jahar Legas a Najeriya.
Mujallar Daily Post ta ruwaito cewa Jami'in tare da abokan aikin sa sun kafa wani wurin binciken ababen hawa akan hanyar tashar Obalage ranar laraba, kuma an bada rahotannion cewar sun karbi kudade da dama daga hannun jama'a musamman masu tuka keke napep.
Suna cikin wannan aiki ne sai kwatsam Ekpo da matarsa akan hanyar su ta dawo wa daga coci suka gogi motar 'yan sandan da aka aje a gefen hanya a yayin da suke kokarin kauce masu.
A sakamakon haka ne sai kawai dan sandan ya budewa mutumin da matar sa wuta ya kuma hallaka matar lahira, wani daga cikin 'yan sanda kuma ya tarwatsa gilashin abin hawan nasu.
Rahotanni sun bayyana cewa Mr Godwin ya sami raunika da dama kuma yana kwance a asibiti yana karbar magani.