Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ya Rasu Yayin Da Ya Ke Aikin Umrah


Alhazai a Umrah
Alhazai a Umrah

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin jihar Katsina Dr. Ibrahim Aminu Kurami ya rasu a kasar Saudiyya da misalin karfe biyu na safe agogon Najeriya, yau Litinin yayin da yake aikin Umrah kuma an yi jana’izarsa a Madina.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Ali Al-Baba, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ko da shike Al-Baba mai wakiltar mazabar Katsina a majalisar bai bayar da cikakken bayani game da rasuwar Kurami ba, ya ce shi da sauran ‘yan majalisar za su kai ziyarar ta’aziyya a garin Kurami da kuma mazabar Bakori na marigayi dan majalisar bayan taron bitar da suke yi a garin Kano.

Kurami dan majalisar wakilai ne na jam’iyyar All Progressives Congress wanda kuma ya lashe zaben fidda gwani na karshe na wakiltar mazabar karkashin jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

An zabi Kurami ne a matsayin dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakilai 34 a zaben cike gurbi na ranar 31 ga watan Oktoba, 2020, bayan rasuwar magabacinsa Abdurrazak Ismail Tsiga.

Marigayin ya bar mata biyu, ‘ya’ya 11, da jikoki uku.

XS
SM
MD
LG