Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waje Road David Moyes - 22/4/2014


Hmm, lokacin da ManU ta tsallake Jose Mourinho ta zabi David Moyes domin zama magajin Alex Ferguson, kungiyar ca-ca fa tayi inda ta zabi Kwach wanda bashi da zuciyar cin wasa, da kwarewa a kwallon kafar turai, da kuma ma rashin kofi ko daya a tarihinsa.

A maimakon haka, United sai ta zabi wanda ya share shekaru 11 a Everton yana kwatanta abun arziki.

Yanzu dai koma ya fito fili, Moyes bashi da ingancin rike ragamar aikin da yafi kowanne girma a wasannin kungiyoyin Ingila, kuma ma hankalinshi ya kwanta da rashin dagewa, kuma ma kamar kungiyar burgeshi kawai takeyi, babu alamar zuciyar kokarin ginata a fuskarshi.

A takaice, mutum ne Moyes wanda yake inda bai kamata ba.

Alal misali, sanda ManU taje away a Liverpool, wasanni uku bayan fara gasar Firimiya na wannan season din, Liverpool ai cinye ManU tayi da 1-0. Kun san ko me Moyes yace?

Cewa yayi wai a ganinshi kungiyar tayi wasa sosai, a dai-dai lokacin da manazarta suke gani kamar kungiyar mai tarin nasarori dingishi kawai takeyi. Yace idan ManU zata ringa wasa kamar haka, to babu shakka zata karashe season din a sahun kungiyoyi hudu na farko a kan teburin Firimiyan.

Ai kuwa hakan akayi tayi.

United ta dauke Moyes daga Everton, amma bata cire Everton daga jikin Moyes ba.
Kafin wasan da ManU tayi a gida da Liverpool, Moyes fa nunawa yayi cewa Liverpool ce zata ci wasan. Shi kanshi Kwac din Liverpool din sai da yayi mamaki, har ma yake cewa ko shine a karkashen teburin ba zai ce haka ba.
XS
SM
MD
LG