Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanda Ya Fi Kowa Yawan Shekaru A Duniya Ya Mutu


Hoton Salustiano Sanchez-Blazquez wanda ya fi duk duniya yawan shekaru kafin mutuwar shi ranar jumma'a ya na da shekaru 112.
Hoton Salustiano Sanchez-Blazquez wanda ya fi duk duniya yawan shekaru kafin mutuwar shi ranar jumma'a ya na da shekaru 112.

Salustiano Sanchez-Blazquez ya mutu ya na da shekaru 112

Mutumin da kundin bayanan ban mamaki da ban ta'ajibi na duniya, wato Guinness World Records, ya amince da cewa shi ne mafi tsufan yawan shekaru a duniya ya mutu. Mutumin mai suna Salustiano Sanchez-Blazquez ya mutu ranar jumma'a a wani gidan ajiye tsofaffi a Grand Island, jahar New York a nan Amurka. Ya mutu ya na da shekaru dari da goma sha biyu a duniya. An haife shi a shekarar Alif Dari tara da Daya a wani kauye mai suna El Tejado do Bejar a kasar Andalusa wato Spain.

Salustiano wanda shi da kan shi ya koyi kida da waka, ya yi kaura zuwa kasar Cuba tun ya na dan saurayi, tare da dan uwan shi da kuma wasu abokan su inda suka yi aiki a gonakin rake.

A shekarar Alif Dari Tara da Ishirin, Sanchez ya taho nan Amurka ta tsibirin Ellis, kuma karshen ta ya yi zaman shi a New York ta bangaren Niagara Falls. Matar Sanchez ta mutu tun a shekarar 1988. Salustiano Sanchez-Blanquez ya mutu ya bar 'ya'ya biyu mace da namiji, da jikoki bakwai, da tattaba kunne goma sha biyar da kuma 'inhihi biyar.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG