Danladi yace yayin da suke shirin komawa teburin shawarwari sun tsagaita wuta. Idan kuma an ji wuta wani wuri to ba daga wurinsu ba ne.
Inji Danladi akwai wasu da ba 'yan Boko Haram bane tare da wasu jami'an tsaro dake aikata ta'adanci da sunan kungiyarsu. Idan barayi sun yi sata ko wasu 'yan iska sun yi barna sai a ce Boko Haram.
Ya kira 'yan Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram su dogara ga Allah. Ya kira shugabannin arewa su san abun da suke ciki. Su dinga kula da na bayansu, musamman talakawa. Rashin kulaawar manyan arewa ya jawo abubuwan dake faruwa. Su daina mugun son kai.
Akan zargin wai wasu 'yan Najeriya ke taimakawa kungiyar Danladi yace tana yiwuwa akwai wasu da suke bada makamai domin su aikata wasu abubuwa na cimma muradunsu amma ba Boko Haram ba.
Amma kamar ya amince cewa tsohon gwamnan Borno shi ya shirya 'yan iska ya basu makami amma ba Boko Haram ba.
Danladi ya bada tabbacin dawo da 'yan matan Chibok da zara an zauna dasu.
Ga karin bayani.