WASHINGTON, DC —
Rayuwa na neman cakudewa zakaran kwallon tamaula Lionel Messi na kungiyar FC Barcelona.
A bayan da aka fitar da kulob din daga gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai, kuma aka ga alamun ba zata kai ba agasar lig-lig na Spain, sai kuma ga labarin cewa a shekara mai zuwa, kungiyar ba zata iya sayen kowane dan wasa ba a saboda hukumcin da FIFA ta yanke mata.
Ana cikin haka, yanzu sai aka fara jin rade-radin cewa watakila kulob din na iya rabuwa da Messi wanda tun yana da shekara 12 da haihuwa take tare da shi. Gidan telebijin na Esports3 yace wasu jigogin FC Barcelona su na kwadayin sayar da shi ga kungiyoyi masu nauyin aljihu irinsu Paris Saint Germain ko Manchester City, matakin da zai iya samarwa da kulob din dala miliyan 250.
A cikin ‘yan kwanakin nan ma, wasan Messi mai shekaru 26 da haihuwa ya fara ja da baya, kuma wadanda suka fi haskakawa a yanzu duk sun fito ne daga kulob din da FC Barcelona ta fi tsana a duk duniya, watau Real Madrid. Wadannan ‘yan wasa dake shanawa a yanzu kuwa sune Cristiano Ronaldo da Gareth Bale