Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar da aka yi ranar lahadi a Turkiyya ya karu zuwa 459. Wasu mutanen su akalla dubu daya da dari uku sun ji rauni.
Ana kyautata zaton adadin wadanda suka mutu zai karu a saboda har yanzu akwai daruruwan mutane, ko ma dubbai, wadanda suke karkashin gine-ginen da suka fada kansu, yayin da wasu dubban ba su da matsuguni.
Jiya talata, ma’aikatan agaji dake neman mutanen da suka kubuta da rayukansu, sun tono wata jaririya mai sati biyu da haihuwa tare da mahaifiyarta da ransu daga karkashin wani gida da ya rushe. Wannan jaririya da uwarta, sun shafe kusan kwanaki biyu karkashin ginin a bayan da wannan girgiza ta rushe gine-gine fiye da dubu biyu. Shi ma mahaifin wannan jaririya yana karkashin ginin amma ba a san ko yana da rai ba.
Kasashe kusan 90 sun yi tayin bayar da agaji, amma Turkiyya ta yi na’am da agaji daga kasashen Iran da Azerbaijan ne kawai, kasashen da su ma su na makwabtaka da yankin da girgizar kasar ta shafa.
Kungiyar agajin Red Cross ta duniya ta ce reshenta na Turkiyya yana kokarin taimakawa wadanda suka kubuta da rayukansu tare da kaiwa ga wadanda ke karkashin gine-ginen da suka rushe. Kungiyar Red Cross ta ce ta raba tantuna fiye da dubu 7 da 500, da barguna dubu 22 da kuma risho da abinci da ruwan sha.
Daruruwan ma’aikatan agaji sun shafe tsawon dare su na aiki da manyan na’urori, su na kokarin kawar da fallayen kankaren gine-ginen da suka fado bisa fatar samo mutane da rayukansu a karkashi.