Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Samun Sabbin Masu kamuwa Da Cutar COVID-19 A Najeriya


Buhari
Buhari

Ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar corona a Najeriya a daidai lokacin da ake ci gaba da rigakafi da wayar da kan jama'a kan hanyoyin kare kai da kai.

Duk da ci gaba da yaki da ake yi da cutar coronavirus a Najeriya, hukumar dake kare yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa an sake samun mutum 45 da suka kamu da cutar a fadin kasar.

Hukumar ta bayyana cewa an samu karin wadanda suka kamu da cutar ne a jihohin Ondo, Lagos, Gombe, Katsina, Rivers da Nassarawa.

A lokacin da shugaba Buhari yake nuna farin cikin samun rigakafin cutar na coronavirus na biyu na allurar AstraZeneca, ya ce ba wata matsala daya da ya samu a jikin sa.

Shugaban wanda damuwarsa ita ce kukan na wasu 'yan Najeriya na amfani da kariyar fuska wanda wasu ke cewa tana hana su numfashi wanda da alamu yanzu zai rage ko daina sawa gaba daya.

Duk da haka jami'an kwamitin yaki da cutar na shugaban kasa na aza alhakin cigaba da bullar cutar kan yadda mutane basa saka takukumin rufe fuska, wanke hannu yadda ya dace, shiga cunkoson jama'a da sauran su, wanda hakan yasa gwamnati ta dakatar da club-club da takaita taruwa a bukukuwa da sauran wurare da mutane ke cunkushewa waje daya.

Manajan ko ta kwana na kwamitin yaki da cutar coronavirus na shugaban kasa Dr. Mukhtar Muhammad ya ce hukumomi da sauran wadanda ke da alhakin yaki da cutar za su ci gaba da sa ido don tabbatar da an bi dokokin da aka saka don kare yaduwar cutar da kuma hukunta duk wadanda suka bijirewa bin dokar.

Zuwa yanzu ar ukunin farko kuma kashi na biyu na rigakafi, an yi wa mutum 1,966,128 wato kashi 97.7 cikin dari.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar:

Har Yanzu Ana Samun Sabbin Masu kamuwa Da Cutar COVID-19 A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00


XS
SM
MD
LG