Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Coronvirus Na Ci Gaba Da Bazuwa A Najeriya


Mai Gwajin COVID-19
Mai Gwajin COVID-19

Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya, (NCDC), ta fitar da alkalumma a kan yakin da take yi da yaduwar COVID-19 a wani sakon Twitter a jiya Litinin.

Sabbin alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa an samu karin daruruwan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.

A cewar hukumar, mutum 648 ne cutar ta harba a ranar Litinin 27 ga watan Yuli, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 41,180.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 18,203 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 860 suka mutu.

An samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 21 kuma har yanzu jihar Lagas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta koronabaros, yanzu ta sake samun mutum 180. Sai jihar Plateau da ke bin ta da mutum 148.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da birnin tarayya Abuja da Karin mutum 44, Ondo - 42, Kwara - 38, Rivers - 32, Oyo - 29, Kaduna - 21, Osun - 20, Edo – 17, Ogun – 17, Ekiti – 11, Kano – 9, Benue – 9, Delta – 9, Abia – 9, Niger – 7, Gombe – 3, Borno – 1, Bauchi – 1, Imo – 1.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:25 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG