UEFA ta sanar da sauye-sauye a gasar zakarun Turai wanda zai fara aiki a shekara 2018/19 karkashin sababbin dokokin da aka amince a gasar shekarar 2018/19, kungiyoyi hudu daga Ingila - da Spaniya, Italiya, da Jamus - zasu sami cancantar shiga kai tsaye a cikin rukuni.
Duk da haka, idan kungiyoyi biyu daga Ingila su ka lashe gasar, to sai tawagar ta hudu za ta koma cikin Europa League. Har ila yau, gasar za ta sake samun sauye-sauyen sababbin lokuta, wasan da ake farashi karfe 7.45pm ya koma 5.55pm da 8 na yamma.
Samun nasara a gasar zakarun Turai - ko Europa League - zai bada damar shiga cikin kungiyoyi 32 na karshe Kai tsaye. Haka kuma Yanzu za a samu kungiyoyi 26 da za su samu tikitin shiga gasar kai tsaye a 2018/19 kamar haka:
Kungiyar da ta lashe kofin zakarun turai da wace ta lashe Europe, Kungiyoyi goma sha shida kuwa daga kasashen Ingila, Spain, Italy da kasar Germany. Sai kuma sauran daga kasashen Portugal, Rasha, Ukraine, France da sauran kasashen da suka can-canta wadanda zasu kasance su cika zuwa kungiyoyi 32.
Kungiyoyi biyu da suka kare a mataki na 5 da 6 a gasar Firimiya zasu samu tikitin shiga gasar Europe kai tsaye, Za a buga gasar karshe na zakarun Turai na 2018/19 a Madrid, na kasar Spain, a ranar 1 ga Yuni.
Facebook Forum