Majiyoyin ‘yan sanda da shaidun gani da idon kamfanin dillancin labaran Reuters sun ce milyoyin mutane ne suka taru domin yin nutso a ruwan kogin mai tsarki a rana mafi sa’a cikin kwanaki 6 na bikin addinin hindu.
Har yanzu ana cigaba da kawo gawawwaki zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na Moti Lal Nehru da ke kusa da wurin fiye da sa’o’i 12 bayan afkuwar hatsarin a taron bil adama mafi girma a duniya, duk da cewar har yanzu hukumomi basu kai ga fitar da adadin mutanen da al’amarin ya rutsa da su ba a hukumance.
An kawo kusan gawawwaki 40 dakin ajiyar gawar, kamar yadda majiyoyin ‘yan sanda 3 suka shaidawa reuters. wani shaidan reuters ya kirga gawawwaki 39 a dakin ajiyar gawar. daya daga cikin majiyoyin ‘yan sandan 3 da wani jami’i na 4 sun ce dukkanin gawawwakin 39 turmutsutsi ne ya kashe su.
“Ana ci gaba da kawo gawawwaki. Muna da kusan 40 a nan. Haka kuma muna sauya musu wuri tare da mikasu ga danginsu daya bayan daya,” a cewar daya daga cikin majiyoyin.
Akwai motocin daukar marasa lafiya 15 a wajen dakin ajiyar gawar sannan fiye da mutane rabin dozen ne ke lekawa domin yin arba da masoyansu.
Sa’ilin da aka tuntube shi, babban jami’in dan sanda Vaibhav Krishna yace ‘yan sanda ba za su iya bada alkaluman ba kasancewar sun shagala da kula da zirga-zirgar mutane.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna