A cikin kokarin da kungiyar mata mai suna sisters saving for paradise ke ci gaba da yi na wayar da kan mata da kuma tallafa masu, a wannan karon kungiyar ta gudanar da taron kuma ta gaiyaci mata domin halattar koyarwa kan watan ramadana daga kwararren malami.
Malam Ibrahim Kalli ya yi tsokaci dangane da batutuwan da aka tattauna a kan su a kwalejin Excell da ke Kano, hajiya Mariya Sanusi Mahadi daya daga cikin wadanda suka shirya taron ta ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu tun bayan shekaru uku da aka fara gudanar da irin wannan koyarwa.
Malamin ya fara ne da cewa mata na bukatar tarbiyya daga wajan iyayen su, da mazajen su da ‘yan uwan su da kuma shugabanni wato gwamnati Kenan da jama’ar gari, dole ne a ba mace cikakkiyar kulawa ta hanyar ilimi da tarbiyya da kuma duk wani abu da zai nuna cewar ana kula da ita.
A kwai bukatar ba mata dama domin su yi amfani da irin tasu baiwar da kuma gudummuwa ga al’umma, sa’annan wajibine kan al’umma, da iyaye da shugabanni, da malamai da kafafen yada labarai su nuna wa al’umma kima da muhimmancin rayuwar ‘ya mace da gudummuwar ta cikin al’umma.
Lallai ne mata su kasance masu tsara abubuwan su domin tafiyar da al’amurran su cikin tsari ba tare da garaje ba, kuma ya zamana cewa tunda Allah ya yi masu baiwa wajan himma da kwazon yin abubuwa to su kasance suna gudanar da komi cikin tsari.
Ga cikakken rahoton.