Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Brazil, Jose Maria Marin, zai tafi gidan yari na shekaru hudu sakamakon cin hanci da rashawa.
Jose Maria Marin, mai shekaru 86, na daya daga cikin jami'an hukumar FIFA bakwai da aka kama a wani hotel a Zurich a watan Mayun shekarar 2015.
An yanke masa hukunci game da amincewa da cin hanci daga kamfanonin kasuwancin na wasanni don musayar kwangila don watsa shirye-shirye irin su Copa America.
Bugu da kari, an ci tararsa dalar Amurka miliyan $1.2, kimanin fan miliyan (£920,000) An yanke masa hukuncin ne a kotun tarayya ta Brooklyn, wadda alkalin kotun Pamela Chen, tayi hukuncin.
kuma shi ne mutum na farko jami'in da aka yanke masa hukumcin a matsayin wani ɓangare na binciken Amurka game da cin hanci da rashawa a hukumar FIFA.
An sami Marin, tsohon gwamnan Sao Paulo, a bara da laifuffuka shida daga cikin bakwai masu alaka da cin hanci da rashawa. Lauyan Marin ya ce zasu daukaka kara kan wannan hukuncin.
Facebook Forum