Real Madrid, ta ce za ta yi tayin karshe kan dan wasan tsakiya na Chelsea dan kasar Belgium Eden Hazard, mai shekaru 27, da haihuwa kafin a rufe cinikayyanr ‘yan wasa na Turai a ranar 31 agusta.
Dan wasan baya na kasar Spain Marcos Alonso, mai shekaru 27, ya ce yana ganin ya kamata ya cigaba da zama a Stamford Bridge duk da cewar Real Madrid da Atletico Madrid na bukatarsa.
Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya nemi mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward, ya sayar da Anthony Martial mai shekaru 22.
Sai dai a nashi bangaren Martial ya yanke shawarar cewa yana so ya zauna a Old Trafford don neman samun dama a fafatawa a bangaren Gefensa na dan wasan gaba.
kungiyar Barcelona, za ta iya dawo da dan wasanta dan kasar Colombia, Yerry Mina daga Everton, kan kudi Euro miliyan 60 kimanin fam miliyan (£53.83m) bayan ta sayar da dan wasan mai shekaru 23 ga kungiyar Everton kan kudi Euro 30.25m (£27.19m) a bana.
Arsenal ta ce ba za ta hadu da dan wasan tsakiyarta Aaron Ramsey, ba kan bukatar da ya nema ta ninka masa albashinsa sau biyu, kamar yadda dan wasan yake so amma sunce suna da amincewar dan kwallo, Wales, mai shekaru 27 zai shiga sabuwar yarjejeniya da kungiyar.
Everton, na son fam miliyan £28m da kari daga kungiyar RB Leipzig kafin ta sanya hannu akan dan wasan Ingila Ademola Lookman mai shekaru 20.
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai Uefa tana shirin gabatar da Mataimakin alkalin wasa na bidiyo, VAR a gasar zakarun Turai. Uefa ta ce zata fara amfani da shi daga wasan kusa da na karshe Quarter final.
Facebook Forum