Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ibrahim Nasiru Mantu Ya Rasu


Marigayi tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu.
Marigayi tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa karkashin tutar jam’iyyar PDP, sanata Ibrahim Mantu ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

‘Yan uwan marigayi Ibrahim Mantu sun bayyana labarin rasuwarsa sa ne da sanyin safiyar Talata, inda suka ce Allah ya yi masa cikawa ne a tsakar daren Litinin, a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da ‘yan uwan margarin suka wallafa a kafar sada zumunta ta WhatsApp, sun ce Sanata Mantu ya yi jinya a gida kafin ciwon ya yi tsanani aka garzaya da shi asibiti, inda rai ya yi halinsa.

Marigayi sanata Ibrahim Mantu dan kasuwa ne kuma dan siyasa, babban jigo a jam’iyyar PDP wanda ya yi fice a siyasar Najeriya.

Mantu ya taba rike kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya a zamanin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

An haifi marigayin Ibrahim Mantu a karamar hukumar Gindiri ta Jihar Filato, kuma rasuwarsa na zuwa ne kwana hudu bayan rasuwar tsohon babban sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya kuma shugaban kwamitin karbar mulki ga shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, Ahmed Joda.

Allah ya jikansa da rahama

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG