Tsohon mai baiwa shugaba Donald Trump shawara kan tsaro, Micheal Flynn, ya amsa laifi yau jumma’a game da yin karya ga hukumar bincike dangane da alakarsa da Jakadan Rasha a Amurka.
Amsa laifin da ya yi ya nuna irin hadin kan da shi Flynn ke bayarwa a binciken katsalandan Rasha a zaben Amurka da mai shigar da kara na musamman Robert Mueller ke yi.
An tuhume Flynn da yin karya kan wata boyayyen tattaunawa da yi da jakadan Rasha na wancan lokacin a Amurka, Sergey Kislyak. A wata takarda da kotu ta fitar ranar jumma’a ya nuna yadda ya tattauna da jakadan kan takunkumin da Amurka ta dora kan Rasha karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama.
Takardar ta nuna cewa a watan Janairu, “da gangan” Flynn ya furta bayanan karya da yaudara ga masu bincike dangane da tattaunawarsa da jakadan Rasha.
Facebook Forum