Tsohon fitaccen dan wasan Brazil Mario Zagallo da ya taba lashe kofin duniya sau hudu ya rasu.
Zagallo ya lashe kofin duniya sau biyu a matsayin dan wasa, sau daya a matsayin koci da kuma sau daya a lokacin da yake rike da mukamin mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Brazil.
Ya rasu yana mai shekaru 92.
Ga ‘yan kasar Brazil, sunan Zagallo daidai yake da kalmomin kishin kasa da samun daukaka a rayuwa.
Shugaban Hukumar Kwallon kafar Brazil, Ednaldo Rodrigues, ya kwatanta Zagallo cikin wata sanarwa da ya fitar a matsayin “daya daga cikin mashahuran ‘yan wasa” na duniya.
Asibitin Barra D’Or da ya yi jinya ya ce a daren Juma’a Zagallo ya rasu bayan da wasu sassan jikinsa suka ki yin aiki.
Dandalin Mu Tattauna