Bincike da bunkasa ilimi fasahar sadarwa a Najeriya na daya daga cikin manyan ayyukan hukumar ta NITDA tun kafuwar shekaru kusan 20 da suka shude, da nufin ganin cewa, kowane dan Najeriya ba’a barshi a baya kan wannan ilimin kimiyyar fasaha da zamani ya zo dashi.
Baya ga haka hukumar ta NITDA ta hada hannu da ma’aikatar ilimin Najeriya wajen tabbatar da cewa, darasin ilimin mikiyyar fasahar sadarwa na cikin manhajar koyar da ilimi.
To amma masu sharhi kan lamuran tsaro sun yi tsokacin cewa, duk da mihimiyyar rawar da na’urorin da ilimin kimiyyar fasahar zamani ya zo dasu, akwai karancin amfani da wadannan na’urori a tsakanin jami’an tsaron Najeriya wajen dakile kalubalen tsaron da najeriya ke fuskanta.
Saurare cikakken rahoton a sauti: