A cikin jawabin da shugaban Amurka Donald Trump yayi wa 'yan Majalisun tarayyar Amurka, yace zai aikawa majalisar da kasafin kudin da fannin tsaro ke dauke da katso mafi tsoka a tarihin Amurka.
Yace sojojin Amurka maza da mata na bukatar wadatattun kayan aiki domin tabbatar da ganin sun gudanar da ayyukan su na kare da kuma hana faruwar yaki, yace muddin idan sojojin Amurka zasu yi yaki to zasu yi ne da niyyar yin nasara.
Yace haka kuma wajibi ne a kashe kudi masu tarin yawa ga tsoffin sojoji domin ko sun sadaukar da rayuwar su, don haka yanzu lokaci ne da za a saka musu.
Sai dai Yace babban burin sa shine ya tabbatar masana’antu sun gudanar da kasuwancin su a cikin Amurka ba tare da wata tsangwama ba wanda har zai kaisu ga barazanar ficewa cikin kasar.
Yace masanaantun Amurka sunfi na kowace kasa biyan haraji a duniya, yace yanzu haka tawagar sa masu kula da harkokin haraji suna nan suna nazarin yadda zasu inganta harkokin haraji ta yadda zasu rage adadiin haraji, ta yadda masana’antu zasu samu saukin gudanar da ayyukan su suma ma’aikata su anfana.
Shugaba Trump yaci gaba cewa, “A halin yanzu idan mun fitar da kayayyakin masanaantun mu zuwa kasashen waje, sai ka taras kasashen da muke kasuwancin dasu su cika mu da dan Karen haraji amma muko idan sun shigo da nasu abinda zamu caje su bai taka kara ya karya ba.’’
Shugaban kuma ya tabo batun dokar shige da fice inda yace, “Yanzu haka gwamnati nayta amsa kiran Amurkawa ta inganta dokokin shiga da fice tare da bunkasa matakan tsaro a bakin iyakokin mu. muddin muka samu damar aiwatar da dokokin bakin iyakokin kaar mu wannan zai taimaka kwarai wajen kara samun abinda ke shigo muna, kana zai taimakawa wadanda basu da aikin yi, kana mu samu damar Karin miliyoyin daloli, wannan shine zai kara sanya al’ummar mu ta zama wurin da kowa zai zauna bada tsangwama ba, domin burin mu shineko wane Ba-Amurkeyayi nasara, ammahakan ba zata samu ba a cikin yanayin da doka da oda basu aiki yadda yakamata, wajibi ne ne mu tabbatar da doka da oda a bakin ikokin kaar mu.’’
Yace don haka ne ya zame wajibi mu himmatu wajen gina babban Katanga a kudancin kasar mu.
Facebook Forum