Dubban ‘yan kasar Venezuela sun dunguma kan manyan titunan Caracas a jiya Laraba, tare da gungun masu goyon bayan Maduro, da kuma masu adawa da shi da manufofinsa na gurguzu.
Jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa a wata unguwa dake yammacin babban birnin kasar. Kuma wani matashi da aka harba a kai a kusa da wurin da aka yi zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, ya rasu a lokaci da yake dakin fida.
An dai dora laifin mutuwar matashin akan bangaren masu goyon bayan gwamnati, da kuma kisan wata mata a San Cristobal. Yanzu haka dai ana gudanar da bincike akan kashe-kashen da aka yi.
An sami rahoton kisan wani dogarin wanzar da zaman lafiya a lokacin zanga-zangar a jihar Miranda, kusa da Caracas.
Idan aka hada mace-macen da suka faru jiya Laraba da kuma wadanda suka faru a cikin makonni 3 da aka kwashe ana zanga-zanga adadin mamatan sun kai 8 kenan.
Facebook Forum