Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Ana Iya Daidaitawa Kan Makomar 'Ya'yan Bakin Haure


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Mai yiwuwa fargabar 'ya'yan bakin haure ta kusa kawo karshe saboda Shugaba Trump ya ce ana iya cimma jituwa tsakaninsa da shugabannin Democrat.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadi jiya Alhamis cewa ya na dab da cimma yarjajjeniya da shugabannin Majalisar tarayyar Amurka saboda kare wasu dubban matasa bakin haure daga barazanar kora, shekaru da dama bayan da iyayensu su ka shigo da su Amurka ba bisa ka'ida ba; ya ce to amma duk wata yarjajjeniyar da za a cimma sai ta hada da gawurtaccen matakin tsaro a kan iyaka.

"To, mu na kan nazarin wani tsari, bisa sharadin samar da gawurtaccen tsarin tsaro a kan iyaka," a cewar Trump a yayin da ya ke shirin tafiya jihar Florida saboda ya gane ma idonsa irin barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Irma ta yi.

Wannan kalamin na Trump ya zo ne ba da dadewa ba bayan da ya rubuta ta kafar Twitter cewa, bai samu cimma wata yarjajjeniya ba da shugabannin 'yan jam'iyyar Democrat a Majalisar Dattawa da ta wakilai, kan batun Dakatar Da Daukar Mataki Kan Yaran Da Aka Shigo Da Su Cikin Amurka Ba Bisa ka'ida (DACA, a takaice), wanda gwamnatin Trump ta soke a makon jiya, ya yin da kuma ya bai wa Majalisar Tarayyar Amurka watanni 6 ta kada kuri'a a kan batun.

Shugabar marasa rinjaye a Majalisar Wakilai Nancy Pelosi da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa Chuck Schumer, sun fadi bayan wata liyafar cin abinci a Fadar White House da Shugaba Donald Trump a daren ranar Laraba cewa sun amince su gaggauta bullo da tsarin kare matasa bakin haure, wadanda su ka yi rajista karkashin shirin DACA, shirin da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya bullo da shi don kare su daga kora.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG