Yayin da ya rage makwanni tara a gudanar da zabe a Amurka, shugaban kasa Donald Trump da abokin takararsa na jam’iyyar Demokrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, jiya Litinin sun dorawa junan su alhakin tashe-tashen hankali kan tituna da ke da nasaba da nuna wariyar launin fata da kuma yadda ‘yan sanda ke muzgunawa ‘yan tsiraru, da suka barke a ‘yan kwanakin nan.
A jiya Litinin Trump ya wallafa a shafin twitter cewa yana shirin kai ziyara a Kenosha ta jihar Wisconsin a yau Talata, inda zanga-zanga ta koma tashin hankali a makon da ya gabata bayan da wani dan sanda ya harbi wani mutum bakar fata a baya yayin da ya ke kokarin kama shi.
An zargi wani matashi farar fata dan banga da ya yi ikirarin kare shaguna a Kenosha, da kashe mutane biyu da kuma raunata na uku a lokacin zanga-zangar a kan tituna.
A lokacin da ya ke nuni da Biden, Trump ya ce tashin hankali a jihar Wisconsin, da rashin zaman lafiya a garin Portland na jihar Oregon da ke arewa maso yammacin Amurka, ya tilastawa “Joe maras kuzari” fitowa daga kasan gidansa a jihar Delaware, inda ya ke yakin neman zaben ranar 3 ga watan Nuwamba, don ya kaucewa taron mutane da yawa a lokacin annobar coronavirus.
A wani jawabi da ya yi jiya Litinin a Pittsburgh, Biden ya dora laifi kan Trump na tashin hankalin da ya barke a sassan kasar, yayin da Amurka ke fama da yaduwar zanga-zanga da a wasu lokuta kan rikide zuwa tashin hankali, da kuma zanga-zangar adawa da yadda ‘yan sanda ke muzgunawa tsiraru da kuma rashin daidaito a cikin jama’ar Amurka.
Facebook Forum