Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dawo daga Faransa gabanin bikin rantsar da shi da za a yi.
A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da sabuwar gwamnatin ta Tinubu, wanda ya lashe zaben 2023 da bangaren ‘yan adawa ke kalubalanta a kotu.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawal, da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da Godswill Akpabio da jam’iyyar APC ta ce a zaba a matsayin sabon shugaban majalisar ta Dattawa ta 10, na daga cikin mukarraban da suka tarbi Tinubu a Abuja.
Kazalika Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje shi ma yana daga cikin wadanda suka tarbi tsohon gwamnan na Legas.
Zababben shugaban kasar ya sauka ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan wani sautin muryoyi da ake zargin Ganduje ne da tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa Ibrahim Masari.
A sautin muryoyin wanda aka kwarmata a shafukan sada zumunta, an ji Ganduje yana korafi kan ganawar da Tinubu ya yi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso.
Yayin da yake Paris, Tinubu ya gana da Kwankwaso.
Kazalika Tinubu ya dawo ne yayin da ake ta takaddama kan shugabannin da za a zaba a majalisar dokoki ta 10.