"Kwarmata tattaunawar sirrin nan tsakanin Flynn da Jakadan Rasha a Amurka kan takunkumin da aka kakaba ma Rasha, ya sa kudurin doka irin wannan ya zama wajibi," abin da wani fitaccen dan Kwamitin Majalisar Wakilai mai suna Adam Schiff ya gaya ma manema labarai kenan a wani taron 'yan jarida da aka kira wajen gabatar da kudurin.
Schiff na magana ne kan tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Janar Flynn, wanda ya ajiye aiki ranar Litini saboda matsin lambar da ta biyo bayan gane cewa Flynn ya yi ta tattaunawa da Jakadan Rasha a Amurka gabanin rantsa da Shugabab Donal Trump.
"Idan dai binciken gaskiya za a yi, to dole ne mu binciki Janar Flynn, dole ne mu yi nazarin abubuwan da tattaunawar ta kunsa kuma dole ne mu kira shi ya yi bayani," a cewar Schiff.
Mai ladabtarwa na marasa rinjaye na jam'iyyar Democrat Steny Hoyer ya ce yayi imanin cewa aniyarsu ta samun goyon baya ainun daga jam'iyyun biyu, ta yadda za a iya gabatar da kudurin ba tare da an yi amfani da ikon yin gaban kai wajen yin watsi da shi ba.