Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas Sai Kotun Koli ta Bada Izini Abun Kuma Zai Dauki Makonni


Lauyan tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na Kudanci Amurka, yace wanda yake karewa wato Nicolas Leoz, na kwance a asibiti domin yana fama da mura.

Nicolas Leoz, dai yana cikin wadanda ake tuhuma da cin hanshi da rashawa a hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Lauya Fernando, yace Leoz, yana mamakin wannan tuhumar, amma a shirye yake ya kare kansa daga wannan tuhumar da ake yi masa.

Ministan harkokin wajen Paragua yace ma’aikatar shi ta karbi takardan neman tasa keyar Leoz, zuwa kasar Amurka, amma yace tilas sai kotun koli ta kasar ta bada izini abunda kuma zai dauki makoni masu zuwa.

Nocolas Leoz, da shekaru 87, ya kasance shugaban hukumar kwallon kafa na kudancin Amurka, daga 1986 zuwa 2013.

A wani labarin kuma, Shugaban hukumar kwallon kafa na Turai, Greg Dyke, yace a halin da ake cikin yakamata Sepp Blatter, shugaban FIFA, yayi murabus domin halin da hukumar ta samu kanta a ciki.

XS
SM
MD
LG