Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, shi ne babban jami’in diflomasiyyar Amurka na farko da ya ziyarci Jamhuriyyar Nijar, a daidai lokacin da kasar ta zama cibiyar tsaro mai muhimmanci ga kasashen yammacin duniya da ke neman tinkarar kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel.