Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Kyauta Tsakanin Saurayi Da Budurwa


Wakiliyar dandalin VOA Baraka Bashir ta tattauna da wata matashiya mai suna Maimuna Muhammad, dangane da rawar da kyauta ke takawa a tsakanin saurrayi da budurwa a lokacin samarta.

Matashiyar ta bayyana ra'ayin ta da cewar, "kyauta na kara dankon zumunci tsakanin saurayi da budurwa, kuma ta jaddada cewar matuka budurwa na soyayya da saurayin da bai bata komi, haka kawai sai taji yana bata mata rai."

Ta kara da cewar, "da zarar saurayi ya fara ba budurwa kyauta, zai sa ta farin ciki matuka, kuma hakan zai sa ta ji tana mataukar kaunar sa."

A ci gaba da hirar, matashiyar ta ce ko a gida idan 'yan uwa suka ga saurayi ya ba 'yar uwar su kyauta, zaka ga suna ta taya ta murna. kyauta ba lallai ta kudi ba, koda irin su turare, ko alewa, ko atamfa ko takalmi da sauran su.

Da zarar saurayi ya ba budurwar sa kyauta, zata ji dadi kuma jama'a za su tabbatar da cewa saurayi ne wanda za'a iya dogaro da shi, iadan aka yi aure da irin sa lallai za'a ji dadi kwarai da gaske.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG