Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Adam Na Iya Rayuwa A Wata Duniyar Kuwa?


Daraktan ilimin kimiyyar duniyoyi na hukumar NASA, Jinn Green ya ce Mars ba duniya bace da take a kekashe a bushe kamar yadda muke zato a da. A wasu al’amura masu tabbatarwa an gano ruwa mai kwaranya a Mars.

A cewar masana kimiyya, in har yadda ake zato haka ne, tuna tabbacin wanzuwar sub a abu ne da yake kai tsaye ba, kananan rafukan zasu kai kimanin fadin kafa 12 zuwa 18, kuma tsawon su zai kai kimanin kafa 300 ko fiye da haka.

Jagaban gwajin na’ura mai fassara hoto karara, Alfred McEwen na jami’ar Tuscon a jahar Arizona ya ce “Abin da muka gani yanzu shine yumbu mai danshi wanda bashi da kauri sosai, ba kwantaccen ruwa ba”.

Saboda ruwa abu ne da yake da muhimmanci ga rayuwa, abin da binciken ya gano zai iya kara jaddada tabbacin samun rai a Mars. A mujallar kimiyyar halittu, masu binciken sun ce akwai bukatar zurfafa bincike don a tabbatar ko mitsatsan halittu na rayuwa a cikin duniyar.

McEwen ya ce shi ya yarda da tabbacin rai a Mars, amma mitsatsan halittu ne, kuma a wani bangare na bangon duniyar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG