Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjejeniya Tsakanin Matasan Musulmi Dana Kirista.


Kungiyoyin matasa da samarin musulmi dana kirista a jihar Kano da kuma kabilu daban daban mazauna Kano sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar zaman lafiya, a yayin zabe da kuma bayan kammala zabukan da za’a gudanar a najeriya.

A gabanin rattaba hannu akan takardar yarjejeniyar sai da aka gudanar da lakcar wayar da kan matasan game da illar shiga harkokin yamutsi musammam ma alokacin zabe, kungiyoyin matasa dana mata da kuma cibiyoyi da kungiyoyin rajin cigaban al’umma ne suka halarci taron. Wadda kungiyar matasan Arewa da hadin gwiwa da kungiyar matasan kiristocin Najeriya reshen jihar Kano, suka shirya, a cibiyar bincike da bada horo kan harkokin dimokaradiyya ta Mambayya a jihar Kano.

Musa Usman shine ya rattaba hannu akan yarjejeniyar amadadin matasan kiristoci rashen jihar Kano, Musa Usman dai yace, so muke da cikin ikon ubangiji da yardar sa wannan karon ayi zabe lafiya, zabe mai kwanciyar hankali da lumana, ya kuma tabbatar da cewa an cimma yarjejeniya an kai ga matsaya kowa ya yarda, wanda a kwai takardun da aka saka hannu cewar matasan kowacce kungiya bazasu zamo sun bada kai ga kowacce irin jam’iyyar siyasa ba, ko dan siyasa domin amfani dasu wajen tada hankula.

Shikuma kwamared Ibrahim Wayyan, wanda ya saka hannu a madadin matasan musulmin Kano, yayi karin haske wanda kunshin yarjejeniyar, inda ya tabbatar da cewa an yarda cewar ‘yan uwa kiristoci zasuje coci domin isar da sakon, mukuma zamuyi amfani da damar mu domin fadakar da matasa musulmi a duk inda suke.

Wannan dai shine karon farko da aka kulla yarjejeniya irin wannan tsakanin matasan musulmi dana kirista da kuma sauran kabilu mazauna Kano.\

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG