Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Agaji Na Kai Dauki Wa 'Yan Gudun Hijiran Libiya

Daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijiran Libiya.
Daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijiran Libiya.

Ganin yadda rikicin kasar Libya ke ci gaba da kazancewa, kungiyoyin bada agaji na kokarin daukan matakan tallafawa farar hular da suka zama ‘yan gudun hijirar dole.

Ganin yadda rikicin kasar Libya ke ci gaba da kazancewa, kungiyoyin bada agaji na kokarin daukan matakan tallafawa farar hular da suka zama ‘yan gudun hijirar dole.

Zancen nan da ake yi garuruwan kan iyakokin Libya cike suke da dubban ‘yan Gudun Hijira, musamman ma’aikata baki ‘yan kasar waje dake aiki a Libya wadanda ke kokarin ficewa su bar kasar Libya, mafi yawansu kuma ‘yan kasashen Afirka ne wadanda mayakan ‘yan tawayen Libya suka fi kaiwa hari. ‘

Yan tawayen na daukan bakar fatar Afirka tamkar sojin hayar da Gadhafi ya kwaso domin su tallafawa mayakansa.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD tayi kiyasin cewa baki ‘yan kasar waje dake aiki a Libya kusan dubu metan da goma sha biyar ne suka tsallaka kan iyakar Libya suka shiga Tunisia da Misra da kuma jumhuriyar Nijer tun 20 ga watan Fabaraiun da ya gabata zuwa yau.

XS
SM
MD
LG