WASHINGTON, DC —
Shugabannin kasashen Afirika suna taro a birnin Abunjan Najeriya kamar yadda wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya shaidawa abokin aiki Bello Habeeb Galadanci.Shugaban Najeriya shi ne ya yi jawabin bude taron inda ya tunashesu cewa a taron shekara 2001 suka fara tunanen yadda zasu shawo kan cututtuka uku a haniyar Afirika.
Makasudin wannan taron na Abuja shi ne yadda Afirika zata yaki cututtuka uku wato sida da tarin fuka da kuma zazabin cizon sauro wadanda suka fi addabar nahiyar Da kuma samuN galaba kansu ba tare da dogara baki daya kacokan kan taimakon kasashen ketare ba.
Kawo yanzu Afirika ta samu nasara kan wadannan cututtukan amma lokaci ya yi da nahiyar zata soma kirkiro magunguna domin yakarsu har ma su samu su sayarwa wasu kasashe dake bukata.
Ga karin bayani.