Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yace tashe tashen hankula, da yawan tsana, da kiyayya, da babbancin launin fata, dake faruwa ayau a duniya suna barazana ga manufofin Majalisar Dinkin Duniya. Yace wajibine a koma kan tafarkin da Majalisar ta tsarawa Duniya.
Shugaba Buhari, yayi wadannan kalaman ne a jawabinsa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Ya fara jawabi da godiya wa babban taron, da karammawa da yayi wa gwamnati da mutanen Najeriya, da ya zabi dan Najeriya kwararran dan diplomaciya Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban taron na Majalisar Dinkin Duniya na 74, .
Muhammadu Buhari, ya bayyana nasarori da gwamnatinsa ta samu, da kuma ayyuka da za ta yi nan gaba. Ya kuma tabo batutuwa da suka shafi kasashen waje, kamar batun Palestinu. Yace ya kamata a baiwa Palestinawa 'yancin su, da kasar su, domin su zauna lafiya ba tare da tsangwama ko tashin hankali ba.
Ya kuma yi jawabi akan ta'adanci dake addabar duniya, da kuma matsalar kasuwanci da ke tsakanin China da Amurka.
A saurari cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Baba Makeri.
Facebook Forum