Cibiyar bincike da bada horo kan harkokin dimokaradiyya ta Mambayya dake Kano ce ta shirya taron, inda masana suka gabatar da kasidu da Makala daban daban kan yadda dimokaradiyya take a Najeriya.
Kwararru da Shehunnan malamai kan harkokin dimokaradiyya da sha’anin tsaro da tattalin arziki daga cibiyoyin nazari ilimi da bincike mai zurfi, harma da jami’o’i da Kwalejoji daga sassa daban daban na Najeriya ne suka hallara inda aka gabatar da kasidun.
Farfesa Haruna Wakili, shine daraktan cibiyar bincike da bada horo kan lamuran dimokaradiyya ta Mambayya, yace cibiyar Mambayya kan zauna duk shekara domin waiwaye kan tafiyar dimokaradiyya domin duba abin da ake ciki musamman kamar ci gaban da aka samu da kuma kalubalen da ake fuskanta da kuma abubuwan da yakamata a gyara.
Shi kuma farfesa Zaiyan M Umar na sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami’ar Usmanu Dan Fodiyo dake Sokoto, ya gabatar da mukala mai take matsaloli da kalubalen kafa turakun dimokaradiyya a Najeriya. inda ya tabo nasarar da aka samu a kasar cikin shekara ta 2007 lokacin da dan takarar jam’iyyar hamayya ya lashe zabe, wanda hakan ke nufin ‘yan Najeriya suna da ‘yancin zabar wanda suke da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki.
Mukalar farfesa Usman Tahar dake koyarwa a kwalejin horas da hafsoshin soja dake Kaduna, ta mayar da hankali ne kan mummunan tasirin da tarzoma rikece-rikice ke yi akan dimokaradiyar Najeriya. inda yace dole ne sai al’umma ta zabi shugabannin na gari dake da kishin kasa domin kawo karshen rikice rikicen dake addabar Najeriya.
Domin karin bayani.